Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta yi watsi da nadin Sarkin Zazzau

Rahotanni daga Najeriya sun ce, Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da rahotan masu zaben sabon Sarkin Zazzau saboda zargin cewar, anyi amfani da kudi wajen sayen kuri’u.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i. The Nation
Talla

Jaridar Premium Times ta ruwaito daga wata majiyar gwamnatin da ke cewa ta yi watsi da rahotan da ke dauke da sunayen masu neman sarautar guda 3, inda aka fara sabon lale domin zabo wanda zai maye gurbin mai martaba Sarki Shehu Idris da Allah Ya yi wa rasuwa a makon jiya.

Jaridar ta ce wannan matakin ya dawo da Ahmed Nuhu Bamalli, daya daga cikin masu neman sarautar kuma na kusa da gwamna Nasir El Rufai cikin ‘yan takarar sarauta, bayan an cire sunansa a  wancan rahotan.

Da wannan mataki, Bamalli da ke rike da mukamin Magajin Gari ya shiga cikin jerin na gaba-gaba cikin masu neman sarautar da suka hada da Iyan Zazzau Bashir Aminu da Yariman Zazzau, Mannir Ja’afaru da Turakin Zazzau, Aminu Idris.

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ya sanar ta shafinsa na intanet cewar, yana dakon shawarar kwamishinan kananan hukumomi da kuma rahotan tsaro kan ‘yan takarar kafin yanke hukunci a kai.

El-Rufai ya kuma sanar cewa, yana ci gaba da karanta littafan da suka shafi tarihi da zaben Sarkin Zazzau domin taimaka masa wajen sauke nauyin da ya rataya a kansa.

Sai dai kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan yace wannan jita-jita ce kawai,kuma su a matsayin su na gwamnati basa aiki da jita-jita.

Aruwan yace gwamnatin jihar Kaduna na aiki bisa ka'aidar doka,kuma suna daukar matakan da suka dace kamar yadda dokokin jihar suka tsara wajen  nada sabon sarkin,inda ya bukaci jama'a da suyi hannkuri,da zaran sun kamala abinda ya kamata,zasu sanarwa jama'a sabon sarkin Zazzau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.