Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun sake sace mutane a Zaria

‘Yan bindiga sun sake kai hari kan wani yanki na unguwar Kofar Gayan low-cost, dake garin Zaria a jihar Kaduna.

Wasu 'yan bindiga a Najeriya.
Wasu 'yan bindiga a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Bayanai daga wasu majiyoyi daga yankin sun ce, ‘yan ta’addan sun afkawa unguwar ce da misalin karfe tara na daren ranar Laraba.

Akalla mutane 10 ake faragbar cewa ‘yan bindigar sun sace yayin harin da suka kai, wanda shi ne tashin hankali karo na biyu da mazauna yankin suka gani.

Sai dai jaridar Daily Trust da ake wallafa ta a Najeriya ta ruwaito cewar mutane 4 daga cikin wadanda aka sace sun tsira daga hannun ‘yan bindigar da suka yi awon gaba da su.

Idan za a iya tunawa a shekarar 2021, gungun ‘yan ta’addan suka kai farmaki kan unguwar ta Kofar Gayan low-cost dake Zaria, inda suka sace wani jami’in hukumar Kwastam da wata mata, kafin daga bisani a sake su bayan biyan kudin fansar da yawansa ya kai kimanin naira miliyan 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.