Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Masu baiwa 'yan bindiga bayanai sun zamewa gwamnati babbar matsala - El Rufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya bayyana miyagun mutanen da ke baiwa ‘yan bindiga bayanai, a matsayin babban kalubalen da ke dakile yunkurin gwamnati na kawo karshen ta’addancin da ya addabi al’ummar jihar.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. © Twitter@GovKaduna
Talla

El Rufa’i ya ce masu baiwa ‘yan ta’adda bayanai, sun zamewa gwamnati da sauran jama’a kadangaren bakin tulu, sakamakon yadda suke boye cikin al’umma ba tare da gano su cikin sauki ba, abinda ya basu damar yin zagon kasa ga matakan kawo karshen ta’addancin ‘yan bindiga.

Gwamnan ya koka ne ranar Asabar a Kaduna, yayin bikin Ranar Tunawa da ’Yan Mazan Jiya ta Najeriya, wanda ake yi ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara domin tunawa da ’yan Najeriya da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare martabar kasar da al’ummarta.

A wata sanarwa da ta fitar kan batun tsaron, gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami’an soji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda uku, a yayin da suke sintiri a hanyar Telele-Sabon Gida a karamar hukumar Chikun da ke jihar.

A cewar sanarwar da Kwamishinan tsaron cikin gidan Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, sojojin sun yi wa ‘yan bindigan kwanton bauna ne a wani wurin da ake zargin matattara ce ta ‘yan ta’adda da ke tafka ta’asa a kan hanyar ta Telele-sabon Gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.