Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

‘Yan ta’addan da suka yi barna a Neja sun kashe mutane 10 a Birnin Gwari

Rahotanni daga arewacin Najeriya sun ce ‘yan ta’addan da suka kai hare-hare kan kauyuka fiye da 20 a jihar Neja, sun kashe akalla mutane 10 a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Yan bindigar sun kuma sace mutanen da ba a tantance adadinsu ba, akasarinsu mata yayin hare-haren da suka kai kan wasu yankunan karamar hukumar ta Birnin Gwari inda suka shafe tsawon sa’o’i suna cin karensu ba babbaka, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar.

Wata majiyar tsaro a yankin ta shaida wa gidan talabijin na Channels da ke Najeriya cewa tun da farko ‘yan bindigar sun kai hari a wasu kauyukan jihar Neja mai makwabtaka da Kaduna ne inda suka yi awon gaba da wasu mutane daga kananan hukumomin Mashegu, Lavun da kuma Wushishi, bayan kashe mutane akalla 17.

Yayin da ‘yan ta’addan ke kan hanyarsu ta komawa sansaninsu ne sai wasu ’yan banga na yankin Birnin Gwari suka kai musu farmaki a kauyukan Ungwan Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga da ke gundumar Randagi a Birnin-Gwari.

Domin ramuwar gayya ne kuma ‘yan bindigar suka koma kauyukan da safiyar ranar Asabar, inda suka kashe mutane goma, da suka hada da ‘yan banga guda shida da kuma mutanen kauyen hudu, tare da yin garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a yayin samamen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.