Jami'ar Ahmadu Bello ta gudanar da zanga-zangar kwace mata filaye
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU reshen Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta gudanar da zanga zangar kin amince wa da kwace wani fili mallakin jami’ar da ya kai kadada100 da gwamnatin jihar Kaduna ta yi domin raba wa alumma da ke bukatar yin gini.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:08
Shugaban kungiyar, Haruna Jibril ya ce wannan abin damuwa ne matuka saboda haka suna kira ga gwamna Nasir E-lrufai da ya gaggauta jenye wannan mataki domin filin makarantar na al’umma ne baki daya. Sai dai a nata bangare, gwamnatin jihar ta ce rashin yin amfani da filin yadda ya kamata tare da sayar da wasu filaye da jami’ar ta yi ne, ya sa ta kwacewa. Wakilinmu daga Kaduna, Aminu Sani Sado ya aiko mana wannan rahoto.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu