Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Yan bindiga sun hallaka Rabiren Dauda bayan kabar kudin fansa a Kaduna

'Yan bindiga sun hallaka wani limamin coci a Kaduna, Rabiren Dauda Bature bayan da suka karbi kudin fansa daga hannun mai dakin sa.

Hukumopmin jihar Kaduna
Hukumopmin jihar Kaduna © Kaduna State Government
Talla

Rahotanni  na nuni cewa,yan bindigan sun yin awon gaba da Rabiren Bature da mai dakin sa ne ranar  8 ga watan Nuwambar da ta gabata a lokacin da yake cikin gonar sa dake yankin Rigasa a karamar hukumar Igabi.

Rabiran John Hayab mataimakin shugaban kungiyar mujami’un arewacin Najeriya da Abuja ne ya sanar da mutuwar Rabiren Bature jiya asabar.

Zanga-zangar jama'ar Kaduna dake neman zaman lafiya
Zanga-zangar jama'ar Kaduna dake neman zaman lafiya REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Kungiyoyi da dama ne a kasar ke ci gaba da kira ga hukumomi domin daukar matakan da suka dace wajen kawo karshen wannan matsala ta rashin tsaro a arewacin Najeriya.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta yiwa illa, abinda ya kaiga asarar tarin rayuka da dukiyoyin jama'a.

'Yan bindiga masu satar mutane domin garkuwa da su da kuma satar dabbobi na ci gaba da haifar da matsala a akasarin jihohin dake yankin arewa maso yammacin Najeriya, abinda ya sa gwamnati katse layukan sadarwa domin baiwa jami'an tsaro damar shiga dazuka domin karkade su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.