Isa ga babban shafi
Kaduna

Kaduna na shirin sallamar daruruwan malaman makaranta

Gwamnatin jihar Kaduna ta Najeriya ta sanar da shirinta na sallamar malaman makaranta har su 233 saboda amfani da kwalin shedar kammala karatu na bogi.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i Twitter@GovKaduna
Talla

Shugaban Kwamitin Zartaswa na Hukumar Bunkasa Ilimin Bai-Daya a jihar, Alhaji Tijjani Abullahi ya bayyana haka a ranar Alhamis a yayin wani taron manema labarai.

Abdullahi y ace, sun gano wannan adadin ne bayan kaddamar da wani aikin tantance sahihancin kwalayen malamai a cikin watan Afrilun bara.

Jami’in ya ce, sun yi haka ne da zummar tabbatar da cewa, malaman na da kwarewar da ake bukata ta karantawa.

Gwamnatin jihar za kuma ta gabatar da wadannan masu kwalayen bogin a gaban shari’a domin fuskantar hukunci kamar yadda Abdullahi ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.