Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Gungun mayakan Boko Haram sun shiga dajin Rijana - Rahoto

Rahotanni daga Najeriya sun ce mayakan Boko Haram fiye da 200 sun fice daga sansaninsu da ke arewa maso gabashin kasar zuwa arewa maso yammaci, domin hada karfi da ‘yan bindiga.

Wasu mayakan kungiyar Boko Haram.
Wasu mayakan kungiyar Boko Haram. AFP
Talla

Bayanan da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito daga wasu majiyoyin tsaro guda 2 a Najeriyar, sun ce bangaren Boko Haram da har yanzu ke biyayya ga tsohon jagoransu Shekau ne ya tura kwamandoji biyu da mayaka 250 zuwa dajin Rijana da ke jihar Kaduna.

Daya daga cikin majiyoyin ya ce gungun mayakan na Boko Haram ne suka kitsa wasu sace -sacen da ake yi a arewa maso yammacin Najeriya a baya bayan nan, yayin da kuma suke ci gaba da horas da ‘yan bindiga wajen sarrafa manyan bindigogin harbo jiragen sama, bama-bamai da sauran muggan makamai.

Har yanzu dai ba a samu jin ta bakin rundunar sojin Najeriya da kuma gwamnatin Kaduna kan wannan al’amari ba.

A watan da ya gabata ‘yan bindigar suka kai hari kan Kwalejin horas da hafsoshin sojin Najeriya ta NDA da ke Kaduna, inda suka yi garkuwa da jami'i guda bayan kashe wasu.

A farkon wannan wata rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da farmaki kan sansanonin ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ke makwabtaka da Kaduna, bayan da aka katse hanyoyin sadarwa a wani mataki na dakile hanyoyin da ‘yan bindigar ke samun bayanai kan ayyukan sojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.