Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

'Yan bindiga sun sake sace mutane a karamar hukumar Chikun

Wasu mazauna yankin Sabon Tasha dake dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, sun gudanar zanga-zangar nuna bacin rai kan fargabar da ta mamaye su a dalilin fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

An dai gudanar da zanga-zangar ta ranar Alhamis ne sa’o’i bayan sace mutane 9 daga Ungwan Gimbiya dake yankin na Sabon Tashar da ‘yan bindiga suka yi a daren ranar Laraba.

Bayanai sun ce daga cikin mutanen da ‘yan bindigar suka sace akwai mai gida da masu hayarsa su 6, kuma tuni maharan suka nemi da a basu naira miliyan 20 domin fansar wadanda suka yi garkuwa dasu.

Tashin hankalin satar mutanen 9 a ranar Laraba ya auku ne kwanaki biyu, bayan harin da ‘yan bindiga suka kai kan makarantar Bethel Baptist dake Maraban Rido a dai karamar hukumar ta Chikun dake jihar Kaduna, inda suka sace dalibai 121.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.