Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Ƙungiyar ƙwadago ta NCL ta janye yajin aiki a Kaduna

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) a Najeriya ta janye yajin aikin gargadi da ta shiga a Jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC yayin yajin aiki a jihar Kaduna, 18 ga watan Mayu 2021
Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC yayin yajin aiki a jihar Kaduna, 18 ga watan Mayu 2021 © NLC
Talla

Kungiyoyin kwadago sun sanar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar kan gwamnatin jihar Kaduna karkashin Gwamna Nasir El-Rufai kan korar ma’aikata da yawan gaske da ya yi.

Yajin aikin ya kawo cikas a jihar

Yajin aikin ya kawo cikas a Kaduna yayin da asibitoci da bankuna da tashar jirgin kasa da filin jirgin sama, da sauransu suka kasance a rufe.

Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC yayin yajin aiki a jihar Kaduna, 18 ga watan Mayu 2021
Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC yayin yajin aiki a jihar Kaduna, 18 ga watan Mayu 2021 © NLC

Gwamnan ya jajirce shugabannin kungiyar kwadagon, yana mai cewa matakin da suka dauka ba zai sa ya sauya matsayinsa kan korar ma'aikatan ba.

To sai dai da yake magana bayan wani taron gaggawa a Kaduna a daren Laraba nan, Shugaban NLC na kasa, Kwamared Ayuba Wabba, ya ce an dakatar da yajin aikin.

Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani

Gwamnatin tarayya ta shiga tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyoyin kwadago.

Da safiyar ranar Laraba, Ministan yada Labarai da Al’adun kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya da takwaransa na kwadago da na ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ta shiga tsakani don magance rikicin.

Gwamnatin tarayya ba ta nade hannu ba kuma tuni Ministan kwadago da aikin yi ya shiga tsakanin hulda gwamnatin jihar Kaduna da kuma kungiyar kwadago. Bugu da kari, hukumomin tsaro a duk fadin kasar sun kuma dauki matakan riga-kafi don tabbatar da cewa 'yan bindiga ba su yi amfani da wannan yanayin ba. Musamman, na san ‘yan sanda sun karfafa sintirin da ke tsakanin Kaduna da Abuja”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.