Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Kaduna: NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki a fadin Najeriya

Kungiyar kwadagon Najeriya ta kasa NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki gama gari a fadin kasar sakamakon abinda ta kira nuna halin ko in kular da gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa’i yayi kan dalilin da ya janyo zanga-zangar ma’aikata bayan shiga yajin aikin gargadin da suka yi.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta kasa NLC, Ayuba Wabba.
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta kasa NLC, Ayuba Wabba. © The Guardian Nigeria
Talla

Tun a ranar Litinin da ta gabata ma’aikata a jihar ta Kaduna suka shiga yajin aikin gargadin na tsawon kwanaki 5, domin bayyana bacin rai da kuma nuna adawa kan matakin gwamnan Kaduna na sallamar ma’aikata kimanin dubu 40 daga bakin aiki, a matakan jiha da na kananan hukumomi.

A ranar Talata shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC na kasa Ayuba Wabba ya jagoranci zanga-zangar adawa da gwamnatin Kaduna, wadda daga bisani ta gamu da cikas, bayan da wasu bata-gari dauke da makamai suka afkawa masu zanga-zangar da zummar tarwatsa su, sai dai hakan ba ta samu ba, saboda gudunmawar jami’an tsaro.

Yayin jawabi jim kadan bayan kammala zanga-zangar shugaban NLC Ayuba Wabba ya zargi gwamnati da daukar hayar ‘yan dabar da suka kai musu farmakin.

A ranar talatar da ta gabata ne dai gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya yi shelanta neman Wabba ruwa a jallo saboda jagorantar gurgunta tattalin arzikin Jihar da yayi da kuma lalata kayayyakin hukuma yayin zanga-zangar da ya jagoranta.

Sai dai shugaban na NLC ya maida martanin cewa babu inda ya tsere dan haka babu bukatar shelanta neman sa ruwa a jallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.