Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

El Rufai ya yi barazana ga kungiyar kwadago game da zanga-zangar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce ba za ta kawar da kan ta daga masu tayar da hankali da sunan kungiyar kwadago ba, wajen katse harkokin kasuwanci da na yau da kullum a fadin jihar.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. © Twitter@GovKaduna
Talla

Gwamnan jihar Malam Nasir El Rufai ya zargi 'yan kwadagon da ke zanga zangar adawa da shirin rage ma’aikata da aikata laifuffukan da suka sabawa dokar kasa, musamman katse wutar lantarki da kai hari kan gine ginen gwamnati da rufe asibitocin jama’a da kuma tilastawa marasa lafiya komawa gida.

El Rufai ya kuma ce ba za su lamuncewa shirin 'yan kwadagon na rufe bankuna da hana 'yan kasuwa gudanar da harkokin su ba, inda ya ke cewa za su dauki matakan da suka dace wajen ganin an dawo da doka da oda cikin Jihar.

Gwamnan ya bayyana neman shugaban kungiyar kwadago na kasa ayuba Wabba da jami’an sa cikin gaggawa domin fuskantar tuhuma a gaban shari’a, yayin da ya ce duk wani ma’aikacin lafiya da yaki zuwa aiki daga matakin albashi na 14 zuwa kasa za a kore shi.

Haka ma ma’aikatan Jami’ar Jihar Kaduna wadanda aka bai wa babban sakataren makarantar tattara sunayen wadanda suka ki zuwa aiki, kamar yadda aka umurci sauran ma’aikatun gwamnati.

El Rufai yace suna kallon yunkurin kungiyar kwadago ta NLC daidai da na Yan bindiga masu satar mutane suna garkuwa da su, inda yake cewa yayin da Yan bindiga ke amfani da harsasai, yan kwadago na amfani da tarin jama’a domin hana mutane gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Gwamnan yace gwamnatin Jihar Kaduna ba zata mikawa wasu Yan tsiraru asusun ajiyar ta ba, kuma zasu cigaba da shirin rage ma’aikata domin daidaita bukatun su a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.