Isa ga babban shafi

Venezuela ta gayyaci Tarayyar Turai a matsayin mai sa ido a zaben kasar

A yau Alhamis ne hukumar zaben kasar Venezuela ta gayyaci kungiyar Tarayyar Turai EU da ta tura da wakilan ta a matsayin masu sa ido a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuli, inda ake sa ran shugaba Nicolas Maduro zai sake tsayawa takara a wani sabon wa'adi.

Zabe a kasar Venezuela
Zabe a kasar Venezuela REUTERS - LEONARDO FERNANDEZ VILORIA
Talla

Elvis Amoroso shugaban hukumar zabe ta Kasa (CNE), ya nuna cewa, an aike da goron gayyata zuwa ga kungiyar tarrayar Turai ta EU, da Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar kasashen Latin Amurka da Caribbean (CELAC), kungiyar kasashe masu tasowa na (Brics), da Tarayyar Afirka.

A wannan makon ne Venezuela ta sanya ranar zaben da aka dade ana jira, wanda ya zo bayan gwamnatin Maduro da ‘yan adawa a Barbados sun amince a gudanar da zabe mai inganci a shekarar 2024 tare da masu sa ido na kasa da kasa.

Nicolas Maduro,Shugaban kasar Venezuela
Nicolas Maduro,Shugaban kasar Venezuela © rfi.fr

Yarjejeniyar dai ta sa Amurka ta sassauta takunkumin da ta kakabawa kasar mai arzikin man fetur a kudancin Amurka, lamarin da ya baiwa kamfanin Chevron da ke Amurka damar ci gaba da hako danyen mai tare da yin musayar fursunoni.

Zaben kasar Venezuela
Zaben kasar Venezuela REUTERS - LEONARDO FERNANDEZ VILORIA

Yarjejeniyar dai ta bukaci a ba ‘yan takarar jam’iyyar adawa damar daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke na hana su rike mukamai.

 Rocio San Miguel,yar adawa a kasar Venezuela
Rocio San Miguel,yar adawa a kasar Venezuela AP - Fernando Llano

Tun daga wannan lokacin, kotun kolin da ke biyayya ga Maduro ta amince da haramcin shekaru 15 kan Maria Corina Machado da ta lashe zaben fidda gwani na 'yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.