Isa ga babban shafi

Jami'an tsaron Venezuela sun karbe iko da gidan yarin da 'yan daba su ka mamaye

Gwamanatin Venezuela ta sanar da nasarar kwace iko da wani gidan yari daga hannun wasu gungun ‘yan daba  da ke da alaka da kasashen duniya, a wani gagarumin farmakin da ya kunshi jami’an tsaronta 11,000.

Jami'an tsaron Venezuela da suka karbe iko da wani gidan kaso da 'yan daba ke amfani da shi a matsayin hedikwata.
Jami'an tsaron Venezuela da suka karbe iko da wani gidan kaso da 'yan daba ke amfani da shi a matsayin hedikwata. AP - Ariana Cubillos
Talla

Gidan yarin na Tocoron ya kasance hedkwatar kungiyar ta Tren de Aragua, inda su ka sanya kayan more rayuwa kamar gidan namun daji, wurin shakatawa da dakunan caca, a cewar wani dan jarida mai bincike da kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi hira da shi kwanan nan.

Gwamanatin Venezuela ta sanar da nasarar kwace iko da wani gidan yari daga hannun wasu gungun ‘yan daba  da ke da alaka da kasashen duniya, a wani gagarumin farmakin da ya kunshi jami’an tsaronta 11,000.
Gwamanatin Venezuela ta sanar da nasarar kwace iko da wani gidan yari daga hannun wasu gungun ‘yan daba da ke da alaka da kasashen duniya, a wani gagarumin farmakin da ya kunshi jami’an tsaronta 11,000. AP - Ariana Cubillos

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin kasar ta taya jami'an tsaro murna kan yadda suka dawo da gidan yarin da ke jihar Aragua na arewacin kasar karkashin ikon gwamnati, inda ta kara da cewa farmakin ya wargaza cibiyar tsara dabarun aikata laifuka.

Shugaba Maduro ya jinjina wa jami'an tsaro

Cikin wata sanarwa shugaba Nicolas Maduro ya yaba da da gagarumar nasarar da aka samu a yaki da kungiyoyin masu aikata laifuka.

Bayan da gwamnati ta sanar da kwace iko da daukacin gidan yarin, ministan cikin gida Remigio Ceballos ya shaidawa kafar yada labaran kasar ta VTV cewa an kai fursunonin zuwa wani wuri na daban.

Fursunoni na rayuwa da 'yan uwansu a kurkuku

Wasu dangi da dama da ke zaune a gidan yarin tare da fursunonin da aka yanke wa hukunci sun taru a waje domin neman halin da ‘yan uwansu ke ciki.

Tawagar AFP ta ga jami'an tsaro dauke da Babura da  Talabijin da na'urorin bada sanyi da microwaves da dumame daga gidan yari.

Da alama wasu fursunoni sun tsere a yayin farmakin, yayin da wata sanarwar gwamnati daga baya ta sanar da cewa za’a fara farautar fursunoni da suka tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.