Isa ga babban shafi

Brazil da Venezuela sun sha alwashin kulla dangantaka mai karfi

Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da takwaransa na kasar Venezuela Nicolas Maduro, sun sha alwashin sake kulla dangantaka mai karfi tsakanin kasashensu, wadda tsohon shugaban Brazil mai ra'ayin rikau Jair Bolsonaro ya katse.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, tare da takwaransa na Brazil, a birnin Brasilia. Ranar 29 ga Mayu, 2023.
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, tare da takwaransa na Brazil, a birnin Brasilia. Ranar 29 ga Mayu, 2023. AP - Gustavo Moreno
Talla

Shugabannin sun sha alwashin ne yayin ganawar da suka yi jiya Litinin a Brasilia, babban birnin Brazil.

A zamanin shugabancin Bolsonaro Brazil ta yanke huldar diflomasiyya da gwamnatin Maduro, tare da shiga jerin kasashe kusan 50 da suka marawa Amurka baya wajen amincewa da jagoran 'yan adawar Venezuela Juan Guaido a matsayin shugaban rikon kwarya, bayan zaben shekarar 2018, wanda masu suka, suka yi watsi da shi.

Sai dai tun bayan komawa kan shugabanci, Lula da Silva ya maido da dangantakar diflomasiyar da ke tsakanin Brazil da Venezuela, a matsayin wani bangare na garambawul din da ya yi wa manufofin kasashen ketaren da tsohon shugaba Jair Bolsonaro ya yi amfani da su.

Babban makasudin ziyarar da shugaba Nicolas Maduro ya kai Brazil dai shi ne halartar taron shugabannin kasashen nahiyar Kudancin Amurka da ke gudana a wannan Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.