Isa ga babban shafi

Iran da Venezuela sun kulla yarjejeniyar hadin guiwa na shekaru 20

Kasashen Iran da Venezuela sun sanar da rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsawon shekaru 20 tsakanin kasashen biyu da ke karkashin takunkumin Amurka.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduru da takwaransa na Iran Ibrahim Raizi yayin wata ziyara a Tehran, 11/06/22.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduru da takwaransa na Iran Ibrahim Raizi yayin wata ziyara a Tehran, 11/06/22. AP - Vahid Salemi
Talla

Kashen biyu sun kulla yarjejeniyar ce ta fannoni da dama yayin ziyarar da shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro ya kai kasar Iran a wannan Asabar.

Shima shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya yaba da kuduri da manyan jami'an kasashen biyu suke da shi na bunkasa alaka a bangarori daban-daban.

Maduro, wanda ke magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a babban birnin Iran, ya ce hadin gwiwar ya shafi bangarorin makamashi da na kudi da kuma "aiki tare kan harkokin tsaro".

Baya ga kasashen irinsu Rasha da China da Cuba da Turkiyya, Iran na daya daga cikin manyan kawayen Venezuela. Kuma kasar na fuskantar tsauraran takunkumin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.