Isa ga babban shafi
Venezuela

Na yi shirin ganawa da Trump- Maduro

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce, a shirye yake ya tattauna da takwaransa na Amurka, Donald Trump wanda ya fara sanar da aniyarsa ta ganawa da jagoran na ‘yan gurguzu.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro. REUTERS/Manaure Quintero
Talla

A yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Venezuela, Maduro ya ce, da zaran lokaci ya yi, a shirye yake ya gana da shugaba Donald Trump cikin girmamawa.

A ranar Lahadi ne shugaban na Amurka da ke zantawa da kafar watsa labaran Axios ya ce, akwai yiwuwar ya yi nazari kan ganawa da Maduro.

Sai dai shugaban ya sauya alkibila a wani sakon Twitter da ya wallafa daga bisani, inda yake cewa, a koda yaushe, gwamnatinsa na tsayin-daka kan ‘yanci da walwala kuma tana fada da gwamnatin zalunci ta Maduro.

Trump ya ce, zai gana da Maduro ne kadai kan abu guda, wato: sauka daga kan karagar mulki cikin girma da arziki.

Amurka dai na cikin kasashen da ke dasawa da shugaban ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, amma goyon-bayan da take nuna masa ya ragu saboda rauni fafutukarsa ta kalubalantar Maduro.

A can baya, Guaido ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Venezuela na rikon kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.