Jagoran 'yan adawar Venezuela na zargin gwamnati da kitsa hari a kan sa
A Venezuela, jagoran yan adawa Juan Guaido ya zargin wata kungiya dake da halaka da gwamnatin Nicolas Maduro da kai masa hari a lokacin da ya kaddamar da rangadi cikin kasar ta Venezuela.
Wallafawa ranar:
Dan adawar a wani faye-fan bidiyo da aka yada ,ya na mai nuna ta yada aka shiya masa kwantar bauna a wani lokaci da ya shirya ganawa a wani gidan cin abinci da wasu magoya bayan jam’iyya mai adawa a birnin San Carlos dake yankin Cojedes a tsakiyar kasar.
Jagoran yan adawa na kasar ta Venezuela na zargin gwamnati da kitsa wannan aika-aika.
Juan Gaido da ya samu tattaunawa ta wayar talho da Shugaban Amurka Joe Biden ranar laraba da ta gabata,na ci gaba da samun goyan bayan kasar ta Amurka,wacce ta ki gayyatar Shugaban kasar Nicolas Maduro a taron kasashen yankin Amurika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu