Isa ga babban shafi
Venezuela

Shugaban Venezuela da mukarrabansa sun take hakkin dan adam - MDD

Wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya samu shugaban kasar Venezuela da laifin cin zarafin bil’adama ta hanyar umarnin kisan gilla ga wasu daidaikun mutane baya ga umarnin azabtarwa a karkashin mulkinsa.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro Juan Barreto/AFP/Getty Images
Talla

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar, na zuwa ne bayan fitar wasu tarin zarge-zarge kan gwamnatin ta Venezuela game da cin zarafin bil’adama, abinda ya kai ga kafa kwamitin bincike don gano gaskiyar batun karkashin hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar.

Rahoton ya bayyana cewa bayaga ministocin gwamnatin ta Venezuela, shi kansa shugaban kasar Nicolas Maduro na da hannu dumu-dumu a umarnin kisan tarin mutane, da kuma cin zarafinsu ta hanyoyi da dama.

Tawagar binciken Majalisar Dinkin Duniyar karkashin Marta Valinas ta ce tun cikin shekarar 2014, shugaban Venezuela tare da mukarrabansa suka bada umarnin yiwa mutane da dama kisan gilla tare da azabtar da wasu.

Rahoton binciken mai shafuka 411 ya bayyana fadar shugaban kasar ta Venezuela, ma’aikatar tsaro da ta shari’a a matsayin wadanda ke kan gaba da suka taka rawa wajen take hakkin bil’adama a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.