Isa ga babban shafi

An samu karuwar mutum miliyan 20 da suka kamu da cutar cancer a duniya - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta koka game da karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar cancer ko kuma sankara duk kuwa da bunkasuwar sassan kiwon lafiya na yiwuwar iya gano alamun cutar tun gabanin kamuwa don bai wa jama’a kariya.

Cutar cancer na ci gaba da ta'azzara dai dai lokacin da kasashen Afrika ke da karancin makaman yakar cutar.
Cutar cancer na ci gaba da ta'azzara dai dai lokacin da kasashen Afrika ke da karancin makaman yakar cutar. AP - Tom Sampson
Talla

Cikin rahoton WHO kan ranar yaki da cutar ta cancer da aka saba gudanarwa a kowacce ranar 4 ga watan Fabarairu, hukumar ta ce daga shekarar 2022 zuwa yanzu akwai akalla sabbin kamuwa da cutar miliyan 20 a sassan duniya baya ga mutum miliyan 9 da dubu 700 da cutar ta kashe.

Rahoton na WHO ya bayyana fargabar yiwuwar alkaluman masu kamuwa da cutar ya karu zuwa mutum miliyan 35 nan da shekarar 2050 wanda ke matsayin karin kashi 77 idan an kwatanta da alkaluman hukumar na 2022.

A cewar rahoton na WHO cutar ta cancer ko kuma sankara ta fi kisa a kasashen da ke fama da matsalar rashin ingantattun asibitocin kula da lafiya da galibinsu ke yankunan Afrika da Asiya.

Rahoton na WHO ya alakanta matsaloli masu alaka da zukar taba sigari da shan barasa da kuma kibar wuce kima a matsayin dalilai na farko-farko da kan haddasa kamuwar da cutar ta cancer musamman ga mutanen da shekarunsu suka haura 18.

WHO ta ce akwai matukar damuwa game da binciken da ta gudanar a kasashe 115 wanda ya nuna galibinsu basu da kayakin kula ko kuma rage radadi ga masu fama da cutar ta cancer ko sankara.

WHO ta ce yanzu haka akwai mutum miliyan 53 da dubu 500 da ke rayuwa da cutar cancer a sassan duniya.

Wani gwaji da WHO ta jagoranci gudanarwa ya nuna cewa ckin nau’ikan cutar ta cancer 36 guda 10 daga ciki ne suka fi ta’azzara tare da kisan mummuke ga duk wadanda suka kamu da su.

Rahoton WHO ya ce cancer huhu ita tafi tsananta da kashi  12.4 sai sankarar mama da kashi 11.6 sannan da cancer ciki da ta hanta kana ta bakin mahaifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.