Kotu ta daure tsohon Firaminista Khan da amaryarsa saboda aure cikin idda
Duniya – Wata kotu a kasar Pakistan a yau ta daure tsohon Firaminista Imran Khan shekaru 7 a gidan yari tare da amaryar sa Busra Bibi saboda abinda ta kira sabawa dokokin Islama wajen gudanar da auren su.
Wallafawa ranar:
Kotun tace amaryar Khan wadda bazawara ce bata cika iddar watanni 3 ba, kamar yadda addinin Islama ya tanada domin sake aure ga wadda mijin ta ya mutu ko kuma ta bar mijin ta na farko.
Tuni jam’iyyar sa ta PTI ta bayyana hukuncin wanda shine irin sa na 3 da aka daure Khan a cikin wannan mako a matsayin na siyasa domin hana shi shiga zabe.
Sai dai lauyan sa Gohar Ali Khan yace zasu daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
A farkon wannan mako, kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 a kan tsohon Firaministan saboda samun sa da laifin bayyana asirin gwamnati, yayin da aka sake yanke masa wani hukuncin na daurin shekaru 14 shi da matar sa Bushra Bibi saboda samun su da laifin cin hanci da kuma sayar da kyaututtukan da aka basu lokacin da yake rike da mukamin Firaminista.
Yanzu haka Khan na tsare a gidan yarin Rawalpindi inda ya kwashe watanni a tsare, yayin da matarsa Bibi da ta gabatar da kan ta ga jami’an tsaro ke tsare a gidan ta dake wajen birnin Islamabad.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu