Isa ga babban shafi

Rasha na kai hare-hare Ukraine da makaman Korea ta arewa da Iran - Amurka

Ukraine ta bayyana cewa har zuwa yanzu ba ta kai ga tabbatar da zargin da Amurka ke yi na cewa Rasha ta yi amfani da wasu makamai da Korea ta arewa ta ba ta wajen kai farmaki Kiev a baya-bayan nan ba.

Wani yanki da Rasha ta kai hari a Ukraine.
Wani yanki da Rasha ta kai hari a Ukraine. REUTERS - VALENTYN OGIRENKO
Talla

A jiya Alhamis ne Amurkan ke cewa ko shakka babu, Rasha na amfani da wasu nau’in makamai ciki har da masu linzami da kuma harsasai wadanda ta samu daga abokananta Iran da Korea ta Arewa, sai dai Ukraine a yau Juma’a ta ce sai bayan gudanar da binciken kwararru ne za ta tabbatar da sahihancin zargin na Amurka.

Fadar White House ta nanata cewa, tabbas Rasha na fama da karancin makamai musamman harsasai sakamakon shekaru 2 da ta shafe ta na yaki a Ukraine.

Kakakin kwamitin tsaron Amurka John Kirby ya bayyana samun taimakon makaman da Rasha ta yi daga Iran da Korea ta arewa wani yunkuri ne na sake zafafa yakin.

A bangare guda kakakin ma’aikatar tsaron Ukraine Yuriy Ignat ya shaidawa manema labarai cewa basu samu hujjojin da ke nuna musu makaman baya-bayan nan da Rashan ta yi amfani da su sun fito ne daga kasashen na Iran da Korea ta arewa ba.

A cewarsa kwararru za su gudanar da bincike kan baraguzan makaman tare da fitar da sakamako.

Korea ta Arewa ta taimakawa Moscow da makamai masu linzami da ke cin zangon kilomita 900 wanda Amurka ke cewa da shi ne Rashan ta kai hari Ukraine a makon jiya wanda ya yi gagarumar barna a yankin Zaporizhzhia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.