Isa ga babban shafi

An samu faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya

Farashin gangar danyen mai ya fadi da kashi 1 a ranar Alhamis, a daidai lokacin da Amurka ta sassauta takunkuman da ta lafta wa Venezuela, domin bata damar fitar da danyen man da take hakowa zuwa kasuwannin duniya.

Wani ma'aikaci da ke aiki a matatar mai ta Druzhba da ke kusa da Nelahozeves, a Jamhuriyar Czech.
Wani ma'aikaci da ke aiki a matatar mai ta Druzhba da ke kusa da Nelahozeves, a Jamhuriyar Czech. © REUTERS/David W Cerny
Talla

Wasu  masu sharhi dai na ganin cewa farashin danyen man bai yi mummunar faduwa bane a sakamakon fargabar da ake yi kan yiwuwar fadadar rikicin Isra’ila da mayakan Hamas, wanda ya janyo ci gaba da ragargaza Zirin Gaza. 

Amurka ta yanke shawarar sassauta takunkuman hana Venezuela sayar da danyan man nata ne da tsawon watanni 6, bayan da a ka cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin kasar da ‘yan adawa kan shirya karbabben zaben shugabancin kasar da na ‘yan majalisu a shekarar 2024. 

Masu bibiyar lamurran dai sun yi gargadin cewa ba lallai bane sassaucin da Venezuelan ta samu ya fara tasiri nan take wajen bunkasa arzikinta na fannin man, sai dai ko shakkah babu, zai bai wa wasu kamfanonin hakar danyen man na kasashen waje, damar komawa filayen da arzikin ke kwance karkashinsu a kasar ta Venezuela. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.