Isa ga babban shafi
Venezuela

Ziyarar Maduro ta farko a waje tun bayan da Amurka ta fara nemansa ruwa a jallo

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya isa kasar Mexico domin halartar babban taron yankin, wanda kuma itace ziyarar sa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan da kotun Amurka ta fara neman sa ruwa a jallo.

Shugaban kasar Venezuela, Nicolás Maduro, ranar 16 ga watan Agusta shekarar 2021.
Shugaban kasar Venezuela, Nicolás Maduro, ranar 16 ga watan Agusta shekarar 2021. Federico PARRA AFP/Archivos
Talla

Ministan harkokin wajen Mexico Marcelo Ebrard ne ya tarbi Mista Maduro a filin jirgin saman kasar, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Mexico ta sanar a shafinta na Twitter.

Tun cikin watan Maris na shekarar 2020, Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta zargi shugaban na Venezuela Nicolas Maduro da "ta'addanci" da fataucin miyagun ƙwayoyi da mallakar makamai, kuma ta sanar da ba da ladan dala miliyan 15 ga wanda ya taimaka aka don kama shi.

Kuma tun daga wancan lokacin, Mista Maduro ya guji barin kasarsa. Wannan tafiya zuwa Mexico ita ce tafiyarsa ta farko a hukumance tun lokacin da tsarin shari’ar Amurka ya tuhume shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.