Isa ga babban shafi
Venezuela

Gwamnatin Maduro na tattaunawa da 'Yan adawa a kasar Mexico

Gwamnatin Venezuela da 'yan adawa sun koma kan teburin tattaunawa a kasar Mexico ranar Juma'a, yayin da abokan hamayyar Shugaba Nicolas Maduro ke neman basu tabbacin gudanar da sahihin zabe domin samun saukin takunkumin.

Shugaban kasar Venezuela da jagoran adawar kasar Juan Guaidó.
Shugaban kasar Venezuela da jagoran adawar kasar Juan Guaidó. YURI CORTEZ, Juan BARRETO AFP/Archivos
Talla

Babbar kawancen 'yan adawa ta sanar a wannan makon cewa za ta kawo karshen kauracewa zaben na shekaru uku tare da shiga zaben magadan gari da na gwamnoni dake tafe a watan Nuwamba.

Matakin ya biyo bayan tattaunawar da bangarorin biyu suka yi a watan da ya gabata da kasar Norway ta shiga tsakani kuma Mexico ta dauki bakuncinsa a kokarin warware rikicin siyasar bangarorin biyu na tswon mulkin shekaru takwas na shugaba Maduro.

Jagoran 'yan adawar Juan Guaido ya fada a wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta cewa:

"Manufar mu ita ce cimma matsaya da za ta warware rikicin ta hanyar gudanar da zaben shugaban kasa da na' yan majalisu cikin 'yanci da adalci."

 

"Duk mun san cewa a yau babu wasu sharuɗɗan gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci a Venezuela. Shi ya sa muka hadu anan Mexico domin tattaunawa, Muna fafutukar cimma waɗannan sharuɗɗan," in ji shi.

Tattaunawar na da manufofi guda bakwai da suka haɗa da sauƙaƙe takunkumi, mutunta haƙƙoƙin siyasa da kuma tabbatar da shirya sahihin zaɓe-amma ba ficewar Maduro ba, wanda 'yan adawa suka zarga da yin magudi a zaɓen shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.