Isa ga babban shafi

Abin takaici ne yadda kasashe ke tseren kera manyan makaman nukiliya- Guterres

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa tseren kera manyan makaman nukiliyar da ke gudana yanzu haka a tsakanin manyan kasashe, wata alama ce ta babbar halakar da ke tunkaro Duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonia Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonia Guterres. REUTERS - Mike Segar
Talla

Guterres a jawabin da ya gabatar yayin kulle taron zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara da aka kammala a birnin New York na Amurka, ya bayyana cewa maimakon kwance muggan makaman nukiliyar, manyan kasashe yanzu haka na gasa ne wajen kera sabbin makaman masu dauke da fasoshin zamani.

A cewar Guterres, wannan mataki babbar barazana ce ga Duniya lura da cewa da zarar wata kasa ta gwada amfani da makamin nukiliyar ko da kuwa a wanne lokaci kai tsaye an kaddamar da yakin nukiliya tsakanin kasashe, wanda kuma zai zama mafi munin bala’i tare da tabarbarewar lamurran jinkai.

Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar wanda ya bayyana wannan tseren sabunta nau’ikan makaman nukiliyar a tsakanin kasashe da rashin hankali, ya ce yanzu haka wadannan manyan kasashe na ci gaba da kara yawan kasafin bangaren tsaronsu musamman China wadda ke daukar wannan mataki shekaru 3 a jere, yayinda tuni wasu kasashe suka fara kwaikwayonta.

A cewar jami’in yawan makaman Nukiliyar da kasashen Birtaniya da China da Faransa baya ga India da Isra’ila dama Korea ta Arewa da Pakistan da Rasha da Amurka suka mallaka ya karu zuwa dubu 12 da 512 a shekarun baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.