Akwai yiwuwar farfado da yajejeniyar nukiliyar Iran - Grossi
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta majalisar dinkin duniya, Rafael Grossi ya ce tattaunawa mai tasiri da ya yi da jami’an Iran na iya share fagen farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Grossi ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya yi tare da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliyar Iran Mohammad Eslami a birnin Tehran.
Ziyarar yini 2 da Grossi ya kai Iran na zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawar farfado da yarjejejniyar nukiliyar 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ta ruguje, duk da cewa akwai alwashin sauke takunkuman karayar tattalin arziki da aka kakaba wa Iran idan aka samu nasara.
A shekarar 2018 Amurka ta janye daga wannan yarjejeniyar nukiliya, kana ta sake kakaba wa Iran takunkumai, lamarin da ya sa Iran ta mayar da martini ta wajen dakatar da aiwatar da alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu