Rasha
Kotun Rasha ta daure madugun adawa
Kotun kasar Rasha ta yanke wa madugun adawa da gwamnati Alexei Navalny hukuncin daurin makwanni biyu a gidan yari, a wani mataki na haramta ma shi jagorantar wani kasaitaccen gangamin adawa a ranar 1 ga watan Maris. Kotun ta kama Navalny da laifin sabawa dokar talla bayan ya lika takardun zanga-zangar shi a birnin Moscow.
Wallafawa ranar:
Talla
Sai dai kafin ‘Yan sanda su tafi da shi, Navalny ya bukaci magoya bayan shi su fito babbar zanga-zangar a ranar 1 ga watan Maris.
Masana na ganin saboda kulle shi da aka yi zanga-zangar ba za ta yi tasiri ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu