Isa ga babban shafi
Haiti

Lantarki ya kashe Mutane a Haiti

A kalla mutane 15 ne suka mutu, baya ga wadanda suka jikkata, a lokacin da wata Wayar Wutar Lantarki mai tsananin karfin gaske, ta fadawa gungun masu jerin gwanon gudanar da bikin nuna al’adun gargajiya na kasar Haiti, da ake kira Carnival a turance  

Mutanen da suka jikkata a hatsarin kwance a Asibiti
Mutanen da suka jikkata a hatsarin kwance a Asibiti cbc.ca
Talla

Hatsarin ya auku ne a daidai lokacin da Dubban mutane suka yi dandazo suna kallon bukukuwan  nuna al’adun gargajiya da aka shiga rana ta  biyu da farawa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa  na AFP ya rawaito daga Ministan kula da yada labarai da al’adun gargajiya na kasar Haiti, Francios Rotchild cewa, Iyalan mutanen da suka mutu na can sun yi zaman dirshan a babbar Assibitin kasar ta Por-oprince domin neman iyalansu, a yayin da Likitoci ke kokarin yiwa wadanda suka jikkata magani.

Akasarin mutanen da yawansu ya kai 80 zuwa 100 da suka je Assibitin domin neman ‘yan uwansu,  na kuka ne a yayin da suke ci gaba da jira.

A dayan bangaren kuma shugaban kasar Michel Martelly, ya gabatar a hukumance, sakon gwamnatin kasar na ta’aziyya ga iyalan mamatan, kuma Gwamnatin na shirin biyan diyya, kuma  za ta dau dawainiyar duk wadanda  suka jikkata a cikin hatsarin.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.