Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila ta kaddamar da sabbin hare hare a Gaza

A safiyar Juma’a sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare akan yankin Gaza a daidai lokacin da ake kyautata zaton cewa Firaministan Benyamin Netenyahu zai jagoranci wanin taron majalisar ministocin kasar domin tattauna sabon shirin tsagaita wuta da sakataren wajen Amurka John Kerry ya gabatar.

Falasdinawa a yankin Gaza da fuskantar hare haren Isra'ila
Falasdinawa a yankin Gaza da fuskantar hare haren Isra'ila REUTERS/Suhaib Salem
Talla

A jiya alhamis wani harin bam da Isrealan ta kai akan ginin Majalisar Dinkin Duniya inda dimbin Falasdinawa suka samu mafaka, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15 cikinsu kuwa har da jami’an Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ke kare jefa dubban mazauna yankin na Gaza a cikin mawuyacin hali.

Kasar Iran ta bayyana cewa ko shakka babu ta taimaka wa ‘yan gwagwarmaya na yankin Gaza da fasaha domin su iya kera makaman da za su kare kansu da Isra’ila, kuma Iran tace tana alfahari da wannan taimako da ta bai wa mayakan.

Shugaban majalisar dokokin Iran Ali Larijani ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce ko baya ga fasaha, Iran na taimaka wa Hamas da kudi da kuma kayan aikin soja domin kare al’ummar Gaza daga barazanar Isra’ila.

Yanzu adadin Falasdinawan da suka mutu sun kai 808 a kwanaki 18 da aka kwashe Isra’ila na kai hare hare a yankin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.