Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan ta kaddamar da hare hare kan ‘yan Taliban

Dakarun kasar Pakistan sun kaddamar da wasu hare hare kan wasu matsugunan mayakan Taliban, lamarin da ya hallaka mutane da dama. Harin na zuwa ne kwana daya bayan wata arangama da aka yi da mayakan na Taliban da suka mamaye filin tashi da saukar jirage dake birnin Karachi.

Harin da mayakan Taliban suka kai a Karachi
Harin da mayakan Taliban suka kai a Karachi REUTERS/Athar Hussain
Talla

Wata sanarwa da sojin kasar suka fitar, ta nuna cewa akalla yankuna guda tara dakarun kasar suka daidaita da sanyin safiyar yau Talata.

Babu bayanai da suka fayyace adadin mutanen da suka halaka a harin, wanda aka kai shi a tsaunukan Khyber.

Wannan hari shine na baya baya nan da dakarun suka kai mafi muni a wannan shekara tun bayan zaman tattaunawa da aka yi da kungiyar Tahreek-e-Taliban wacce ta ruguje daga baya.

A fadan na Karachi wanda aka yi a ranar litinin, mutane 30 ne suka rasa rayukansu yayin da bayanai ke nuna cewa dubban mutane suka tsere daga gidajen su a yankunan na ‘yan taliban gudun faruwar azal na daukan fansa.

Mutane da daman a ganin wannan harin da kungiyar Taliban ta kai a jiya, ya kawo karshen yunkurin da ake yi na samar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da yan kungiyar ta taliban a kasar Pakistan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.