Isa ga babban shafi
Pakistan

Mutane 28 sun mutu a fadan Taliban da sojin Pakistan

A kalla mutane 28 aka tabbatar da mutuwar su, sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin sojan Pakistan da ‘Yan kungiyar Taliban, da suka mamaye filin jirgin saman birnin Karachi. Wannan ya jefa dan karamin zaman lafiya, da aka samu a kasar ta Pakistan cikin halin rashin tabbas.  

Wasu 'Yan kungiyar Taliban
Wasu 'Yan kungiyar Taliban REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Mayakan na Taliban sun isa filin jirgin saman Jinnah, a birnin Karachi da misalin karfe 12 na dare jiya Lahadi, dauke da makaman da suka hada da bindigogi, makaman harbo jiragen sama da rigunan kunar bakin wake, inda suka karbe filin na wani lokaci.

Jami’an gwamnatin kasar sun ce dukkan ‘yan bindiga 10 da suka kai harin, suna daga cikin mutanen da suka mutu, bayan akalla 3 daga cikin su sun tayar da bama baman da ke jikinsu.

Sauran mutane 18 da harin ya rutsa da su, sun hada da masu gadin filin jirgin su 11 da ma’aikatan kamfanin jiragen saman kasar ta Pakistan 4, baya ga wasu mutane 26 da suka sami raunuka.

Kungiyar Tehreek-e-Taliban Pakistan, da ta dauki alhakin kai harin ta ce wannan ne na baya bayan nan, a jerin hare haren da take kaiwa, a matsayin fansar mutuwar shugaban kungiyar, Hakimullah Mehsud, daya mutu sakamakon wani harin da kuramen jiragen saman Amurka suka kai a kasar a watan nuwamban bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.