Isa ga babban shafi
Chile

Michelle Bachelet ta lashe zaben shugaban kasa a Chile

An zabi Michelle Bachelet mai ra’ayin gurguzu a matsayin sabuwar shugabar kasar Chili bayan samun rinjayen kuri’u tsakaninta da abokiyar takararta. A lokacin yakin neman zabenta ta yi alkawali samar da daidaito tsakanin attajirai da kuma masu karamin karfi a kasar.

Michelle Bachelet tana murnar lashe zaben shugaban kasa a Chile.
Michelle Bachelet tana murnar lashe zaben shugaban kasa a Chile. REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

Bachelet ‘Yar shekaru 62 a duniya, za ta karbi ragamar mulkin kasar ne a ranar 11 ga watan Mayun badi daga hannun shugaba Sebastian Pinera, domin yin mulki na tsawon shekaru 4.

Bayan kirga Kuri’u kashi 90 da aka kada a zaben, Bachelet ta samu kashi 62 na kuri’u yayin da abokiyar hamayyarta Evelyn Matthei tsohuwar Ministan kwadago ta samu kuri’u kashi 38.

Bachelet ta taba zama shugaban kasa tsakanin 2006 zuwa 2010, inda a yanzu a tarihin kasar ita ce shugaba ta farko a Chile da zata yi wa’adi na biyu tun zamanin mulkin Soji na Janar Augusto Pinochet da ya shata mulki tsakanin 1973 zuwa 1990.

Bachelet ta kulla kawance da sauran Jam’iyyun siyasa na addini a kasar inda ta sha alwashin samar da daidaito tsakanin masu hannu da shuni da attajirai a Chile.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.