Isa ga babban shafi
WHO

Hukumar Lafiya ta Majalisar dunkin Duniya ta ce ana zagon kasa ga gangamin lahanin Taba Sigari

Hukumar Lafiya ta Majalisar dunkin Duniya ta zargi babban Kamfanin sarrafa Taba Sigari Philip Morris akan kokarin yin zagon kasa ga matakan da kungiyar tarayyar Turai ke dauka na rage karfin Kasuwar Taba Sigari, domin ceto Mata da Matasan yankin daga zukar Taba da suke.

Taba Sigari
Taba Sigari galaxyelectroniccigarette.co.uk
Talla

 Wannan batun na gurgunta kasuwar Taba Sigari da kungiyar tarayyar Turai ke yi, wani mataki ne na cika kudurin Majalisun Dokin yankin Nahiyar Turai kan gangamin da masana harkokin kiyon lafiya ke yi na cewar Taba Sigari na lahanta mutane, kuma yin hakan zai ceto rayukan mutane da dama.

Babbar Darakta a hukumar lafiyar ta Majalisar dunkin Duniya Margaret Chan ta bayyana cewar yanzu haka masu kamun Kafa da dama na can suna kokarin hana amincewa da kudurin Dokar.

Babban Misali a nan inji Daraktar shi ne yanda suka ga shi kanshi mai Kamfanin, Phllip Morris ke ta kokarin yin zagon kasa ga wannan yunkuri na kasashen Turai.

A Satin daya gabata ne dai Majalisar Turai ta kai batun zaben har zuwa Watan Okotoba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.