MDD tace ‘Yan Tawayen Kony sun kashe yara 600
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kungiyar Yan Tawayen Lords Resistence Army, da sace yara kana 600 wadanda aka tilasta musu aikin soji a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Jami’in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kananan yara da ke yankunan tashin hankali, Radhika Coomaraswamy, yace yawancin yaran da ake kamawa, akan tilasta musu kashe ‘Yan uwansu.
Rahotan yace, ‘Yan Tawayen Joseph Kony sun kashe yara 45 daga shekarar 2009 zuwa 2012, yayin da kuma suka kama yara kanana 591 da kuma mata 268 a kasashen Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Afrika ta Tsakiya, da kuma Sudan ta kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu