Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Syria ta yi watsi da kalaman Ban Ki-moon

Gwamnatin Bashar al Assad na Syria ta bayyana bacin ranta ga kalaman Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, wanda yace kasar ta kama hanyar fadawa yakin basasa, a dai dai lokacin da wa’adin da ‘Yan Tawayen kasar suka bayar ke kawo karshe.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Talla

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Syria, Jihad Makdisi, yace Ban Ki Moon, ya kauce daga matsayinsa na mai tabbatar da zaman lafiya a duniya, zuwa mai iza wutar yaki.

Jami’in yace, binciken da suka gudanar, ya nuna musu, ‘Yan Tawaye ne suka hallaka mutane 108 a Houla, da ake zargin dakarun gwamnati da aikatawa.

Mista Ban yace, rahotan da ya samu daga Kofi Annan, ya nuna kasar Syria na cikin tsaka mai wuya.

Ban yace Kisan gilla kan fararen hula, zai jefa Syria cikin yakin basasa, wanda kasar ba zata iya farfadowa ba.

Ban Ki-moon ya yi kira ga Syria ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da Kofi Annan ya shata.

A nata bangaren Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton tace, kasar Rasha ce mai ba kasashen Duniya ciwon kai a yunkurinsu na sasanta rikicin Syria.

A cewar Clinton suna fuskantar adawa daga Rasha da China, saboda za su ci gaba da matsin lamba ga kasashen domin ganin sun tirsasawa Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.