Isa ga babban shafi

Wani mahari ya caka wa jagoran 'yan adawar Korea ta Kudu wuka a wuya

Rahotanni daga Korea ta Kudu na cewa an samu wani mugu da yayi kwance-kwance tare da caka wa jagoran jam'iyyar adawa a kasar Lee Jae-myung wuka a wuya, a lokacin da yake zantawa da manema labarai yau Talata a birnin Busan.

Jagoran 'yan adawar Korea ta Kudu Lee Jae-myung kwance cikin mawuyacin hali bayan caka masa wuka da aka yi a wuya a garin Busan.
Jagoran 'yan adawar Korea ta Kudu Lee Jae-myung kwance cikin mawuyacin hali bayan caka masa wuka da aka yi a wuya a garin Busan. via REUTERS - YONHAP
Talla

Lee na tsaka da tafiya ne a tsakanin tarin 'yan jarida bayan da ya ziyarci wurin da aka gina wani sabon filin jirgin sama, a lokacin da aka yi masa aika-aikar, inda nan take ya fadi kasa, kamar yadda hotunan bidiyon da gidajen talabijin da dama na Korea ta Kudu suka nuna.

Hotunan sun da suka yadu dai sun nuna yadda jami’an ‘yan sanda da jama’ar da ke wurin suka afka wa maharin, yayin da saura suka ruga kan Lee Jae-myung domin taimaka masa.

Jagoran jam'iyyar adawa ta Democrat dai ya fafata a zaben neman shugabancin Japan na shekarar 2022, inda ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Yoon Suk Yeol.

Kafin harin da aka kai masa, Lee Jae-myung na fuskantar shari'a bisa tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa dangane da wani kamfani da ake zargi da aika kudaden da yawansu ya kai dala miliyan 8 ba bisa ka'ida ba zuwa Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.