Isa ga babban shafi

Shugaban Koriya ta Arewa ya isa Rasha don ganawar sirri da Putin

Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un ya isa Rasha don gudanar da wani taro da takwaran sa Vladmir Putin, yayin da ya sami rakiyar manyan masu bashi shawara kan kerawa da kuma tabbatar da cewa kasar ta mallaki makamin nukiliya.

Babu wani takaiman bayani a game da abinda shugabannin biyu zasu tattauna
Babu wani takaiman bayani a game da abinda shugabannin biyu zasu tattauna © Yuri Kadobnov / AP
Talla

Bayanai sun ce Shugaba Kim ya shiga Rasha ne ta jirgin kasa, don halartar wannan “shu’umin taro” kamar yadda kasashen yammacin duniya suka kira shi.

Duk da babu wani cikakken bayan akan dalilin wannan ziyara ko kuma abinda zasu tattauna yayin ganawar, amma dai ana zargin watakila ba zata rasa nasaba da neman goyon bayan Rasha wajen tabbatuwar samun makamin nukiliya da kasar ta dade tana nema ba.

Da yake jawabi Jeon Há Gyu kakakin ma’aikatar tsaron Koriya ta Kudu ya ce kafin halartar shugaban, sai da aka tura tawaga ta musamman cikin wannan jirgin kasa don yin shawagi a hanyar da zasu bi don isa Rasha da nufin tabbatar da tsaron ta.

Ta cikin wata sanarwa da fadar Kremlin ta wallafa a shafin ta na Internet tace Shugaba Putin ne ya gayyacin Kim kuma zasu gudanar da wannan ganawa cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ba tare da bayyana takamaimai ranar ko wajen da za’a yi ganawar ba.

Tuni dai kasashen yammacin duniya suka fara nuna shakku game da wannan ganawa, da suke ganin zata iya shafar manufofin su, musamman kan samar da makamin nukiliya ko kuma yakin da Rashan ke gwabzawa da Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.