Isa ga babban shafi

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami da ba a tantance irinsa ba

Korea ta Arewa ta harba makami masu linzami cikin teku na gabashin kasar a Lahadin nan, kwana guda bayan da sojin korea ta Kudu da na Amurka suka  kammala wata gagarumar rawar daji tare a karon farko cikin shekaru 4.

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un Reuters/路透社
Talla

Korea ta Arewa ta kara azama wajen shirin inganta makamanta a cikin wannan shekarar, duk kuwa da cewa tana fama da takunkuman karayar tattalin arziki.

Babban hafsan hafsoshin sojin Korea ta Kudu ya ce sun gano makamai masu linzami 8, masu cin gajeren zango da Korea ta Arewa ta harba a tekun gabashi na kusa da Japan.

Japan ta tabbatar da lamarin, inda ta ce Korea ta Arewa ta yi gwajin  makamai masu linzamin ne a  yankuna da dama, tana mai cewa kasar ta yi gwaje gwaje da dama na makamai a wannan shekarar fiye da yadda ta taba yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.