Irrfan Khan: Masana'antar fina-finan India ta rasa babban jarumi
Fitaccen jarumin fina-finai dan kasar India, da ya taka rawar gani a fim din "Slumdog millionaire" Irrfan Khan, ya mutu yau yana da shekaru 53 a duniya, bayan fama da cutar kansa tsawon shekaru 2.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hazikin jarumi Irrfan Khan ya bayar da gagarumar gudunmawa a masana'antar fina-finan Indiya ta Bollywood har ma da Hollywood ta Amurka, inda yayi suna cikin fim din 'Jurassic World'.
Bayanai sun ce tun a shekarar 2018 likitoci suka tabbatar jarumin ya kamu da cutar kansa.
Khan haifaffen yankin Rajasthan na India ne, wanda kawo yanzu ya fito a fina-finai fiye da 100, yayi kaurin suna ne a fina-finai irinsu ‘Slumdog millionaire’ da ‘Life of Pi’ da kuma ‘Amazing Spider Man’.
Jarumin ya mutu ya bar yara guda biyu.
An haifi Irrfan Khan a ranar 7 ga watan Janairun shekarar 1967, kuma tun yana karamin yaro ya nuna sha'awar ba da gudunmawa a masana’antar fina-finai ta Bollywood inda ya shigar makarantar koras da ‘yan fim ta ‘National Scholl of Drama’ dake India.
Khan ya samu horo na musamman a bangaren wasannin Hikaya, dalilan da suka saukaka masa damar samun gurbi a masana'antar Bollywood cikin sauri.
Sai dai Irrfan Khan ya gaza samun cikakkiyar karbuwa a wanccan lokacin la'akari da yadda masana'antar dungurugum ta karkata wajen baiwa bangaren raye-raye muhimmanci, sashin da Irrfan bai da cikakkiyar kwarewa a kansu.
Bayan taka rawa a kananan fina-finai a shekarar 2001 ne tauraruwar Irrfan Khan ta fara haskawa yayinda aka fara sanya shi a sahun manyan jaruman masana'antar ta Bollywood.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu