Isa ga babban shafi
Lebanon

Lebanon ta karbi kayan yakin da Saudiya ta siya mata

Kasar Lebanon ta karbi zangon farko na makaman da Saudi Arabiya ta saya wa dakarun kasar, don tunkarar yaki da ta’addanci, musamman kan iyakar kasar da Syria

Makaman yaki
Makaman yaki
Talla

A baya, wasu kasashen yammacin duniya sun yi ta taimaka wa Lebanon din da kayan aikin soja, a kokarin da take yi na yaki da masu tatstsauran ra’ayi

 

Makaman da suka isa Lebanon sun hada da na kare makamai masu linzami, da aka mika su ga hukumomin, a wani filin jirgin saman soja dake birnin Beirut.

Ministan Tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ne ya raka makaman, da aka sayo kan kudin da ya kai Dalar Amurka Biliyan 3, daga Faransa.

Le Drian ya ce, Faransa da Lebanon suna da dangantaka mai karfi, sakamakon yadda harkokin tsaro ke tabarbarewa a Levant, da ke zaman baraza ga harkokin tsaron yankin gabas ta tsakiya.

Ana sa rai cikin shekaru 4 masu zuwa, Faransa zata baiwa Lebanon kayan yakin da suka hada da motocin yaki 250, motocin sufuri jiragen sama masu saukar ungulu 7, kananan jiragen ruwan yaki 3, da sauran kayan bincike da na sadarwa.

Kwangilar ta kuma kunshin bayar da horo na tsawon shekaru 7 ga sojan Lebanon dubu 70, da gyaran kayan aiki na tsawon shekaru 10.

Kasar saudiyya data dauki nauyin biyan kudin kayan yaki na da dangantaka ta kut da kut da manyan ‘yan siyasan kasar Lebanon.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.