Isa ga babban shafi
Lebanon

Hezbollah na yaki da Mayakan IS a Iraqi

Shugaban Kungiyar Hezbollah ta Lebenon Hassan Nasrallah ya ce mayakansa na yaki a kasar Iraqi don murkushe mayakan IS da ke da’awar Jihadi a kasar. Wannan ne karon farko da shugaban kungiyar ya bayyana cewa suna yaki da IS a Iraqi.

Hassan Nasrallah na Hezbollah ta Lebenon
Hassan Nasrallah na Hezbollah ta Lebenon REUTERS/Khalil Hassan
Talla

Nasarallah ya ce duk da ya ke a baya ba su ce uffan ba kan yakin saboda halin da kasar ke ciki, amma suna da mayaka a cikin Iraqi.

Shugaban na Hezbollah ya ce dakarunsu na samun galaba tare da sojojin Bashar al Assad a yakin da suke a kasar.

Kalamansa kuma na zuwa ne bayan Firaministan Lebanon Saad Hariri ya yi kira ga Hezbollah ta gaggauta ficewa daga Syria.

Masana dai na ganin kungiyar Hezbollah da ke bin Shi’a ta shiga yaki a Iraqi ne saboda banbancin akida tsakaninta da IS masu bin Sunni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.