Japan tace har yanzu ba a kulla yarjejeniya ba don sako mutanen da ISIS ta kama
Hukumonin kasar Japan sun ce har yanzu ba a kai ga kulla yarjejeniya da ‘yan kungiyar ISIS ba, da suka yi barazanar hallaka wani matukin jirgin sama da kasar Jordan Maaz al-Kassasbeh, da kuma dan Jaridar kasar ta Japan Kenji Goto. Ministan harkokin wajen kasar Yasuhide Nakayama, dake jagorantar tawaggar agajin gaggawan kasar, ya shida wa ‘yan jarida a birnin Amman na kasar Jordan cewa har yanzu ba a sako mutanen 2 ba.Can a birnin Tokyo kuwa, yau Asabar wani babban jami’in gwamnatin Japan Hiroshige Seko, dake a matsayin na hannun dama Fraiminista Shinzo Abe, yace suna dakon bayanai kan halin da mutanen ke ciki.Jiya wa’adin da mayakan na ISIS suka bayar ya cika, inda suka nemi a sako wata mace ‘yar kunar bakin wake dake tsare a gidan yarin kasar Jordan ko su kashe mutanen 2.A makon da ya gabata mayakan na ISIS suka fille kan wani dan kasar Japan mai suna Haruna Yukawa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: