Saudiya ba za ta rage yawan Man da ta ke fitarwa ba
Kasashen Larabawa masu arzikin mai sun ce ba zasu rage adadin man da suke fitarwa ba a kasuwa saboda faduwar farashin man a kasuwannin duniya, duk da wasu kasashen da ba su cikin kungiyar OPEC sun nemi rage yawan danyen man da ake fitarwa.
Wallafawa ranar:
Saudiya da Kuwait masu arzikin mai sun ce ba za su rage yawan adadin man da suke fitarwa ba, yayin da kuma Daular Larabawa da Iraqi suka yi watsi da kiran da ake yi wa OPEC akan ta kira taron gaggawa game da faduwar farashin mai.
Amma a wani taron makamashi da aka gudanar a birnin Abu Dhabi na Daular Larabawa, Ministan mai na Saudiya Ali al Naimi ya jaddada cewa Saudiya ba zata rage yawan adadin man da ta ke fitarwa ba, kuma Ministan Kuwait ya amince da hakan.
An dai samu faduwar farashin danyen mai ne a kasuwannin duniya da kusan kashi 50 tun a watan Yuni, saboda wadatuwar man a kasuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu