Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Iran na shirin taimaka wa Paladinawa da makamai

A daidai lokacin da aka share kusan kwanaki 50 Isra’ila na kai hare-hare a zirin Gaza, kasar Iran ta ce za ta taimakawa Palasdinawa da makamai domin kare kansu.Matakin na Iran dai ya zo ne kwana daya bayan da kasar ta sanar da harbo wani jirgin leken asirin Isra’ila a kusa da cibiyar nukiliyar kasar da ke Natanz.  

Janar Amir Ali Hajizadeh, kwamandan dakarun juyin juya halin musuluncin Iran.
Janar Amir Ali Hajizadeh, kwamandan dakarun juyin juya halin musuluncin Iran. Irna
Talla

Babban kwamandan askarawan juyin juya halin musuluncin kasar ta Iran Janar Amir Ali Hajizadeh, ya ce bayan da Iran ta harbo jirgin leken asirin Isra’ila a kusa da cibiyar nukiliyarta da ke yankin Natanz, a yau kasar na da damar mayar da martani da duk irin matakan da ta ga sun dace.

Ko a cikin watan da ya gabata, jagoran juyin juya halin musluncin kasar Ayatullahi Ali Khamenei, ya fito fili ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wa al’ummar Palasdinu da makamai domin kare kansu daga abinda ya kira kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa mazauna yankin.

A jiya lahadi ne dai hukumomin na Iran suka bayyana cewa wani jirgin leken asiri maras matuki na Isra’ila ya yi kokarin ratsa sararin samaniyar cibiyar da ke Natanz to amma an harbo shi.

Har zuwa yau Iran ba ta yarda cewa akwai wata kasa mai suna Isra’ila ba a duniya, kuma kimanin shekaru 2 da suka gabata, Yahudawan na Isra’ila sun yi barazanar kai wa cibiyoyin na nukilyar Iran hari domin lalata su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.