Isa ga babban shafi
Iran-IAEA

Iran ta ki amincewa shigar Jami’an IAEA a Hukumar tsaronta

Kasar Iran ta ki amincewa da shigar masu binciken Nukiliya na Majalisar dunkin Duniya a babbar Hedikwatar Sojin kasar da ke a wajen birnin Tehiran da manufar yin bincike kan matakan Sojin da kasar ta Iran ke dauka

news.yahoo.com
Talla

Tun dai a shekarar 2005 ne masu bincike ke kokarin kai jiki a harabar babbar Hedikwatar tsaron kasar ta Iran, da ita kuma Iran ta ce sam ba za ta sabu ba.

Sai dai kamin shekarar ta 2005 Hukumar ta sha kai ziyara a babbar Hedikwatar tsaron ta Iran amma bata samu komai na hatsari da kassahen Duniya ke fargaba akan ita kasar Iran ba a Hedikwatar tsaron.

A wani labarin kuma kasar Iran ta buda Kamfanin sarrafa Makamashin Uranium da zai samar da Sinadarin da za’a yi amfani da shi domin samar da Tashar Nukiliya.

Babban Jami’in kula da Hukumar samar da Makamashin Aton kasar Ali Akbar Saleh y ace Kamfanin da aka buda a Esfahan da ke tsakkiyar Iran na samar da fasahar sarrafa Makamashin Uranium da bai kai sama da kashi biyar ba, domin tabbatar da an yi dai dai da bukatun Manayan kassahen Duniya kan batun Nukiliyar kasar ta Iran.

Nan da ranar 25 ga Watan Agustan da muke ciki dai Iran zata gabatar da Rahoto a gaban hukumar kula da yaduwar Makamin Nukiliya ta Majalisar dunkin Duniya IAEA domin tabbatar da ko Iran ta bi Sahun yarjejeniyar da Manayan kassahen Duniyar suka yi da ita ko A’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.