Isa ga babban shafi
Saudi

Saudiya ta fille kan mutane biyu

Mahukuntan kasar Saudiya sun fille kan wasu mutane biyu da Takobi bayan yanke masu hukuncin kisa, inda a bana adadin mutane 28 ke nan a ka zartarwa hukuncin kisa a kasar. Kamfanin dillacin labaran Saudiya yace an fille kan Yussef al Nafili a garin Taif bayan kama shi da lafin bindige Salman al-Rabii mutumin Saudiya.

Sarki Abdallah na Saudiya
Sarki Abdallah na Saudiya AFP/Getty Images)
Talla

Mutum na biyu kuma, Abdessalam al-Ruili an fille kansa ne a garin Arar yankin arewacin Saudiya, kamar yadda ya kashe Abdessalam al Anzi da wuka.

A bara dai kimanin mutane 78 gwamnatin Saudiya ta zartarwa hukuncin kisa, karkashin tsarin dokar kasar ta Shari’ar Musulunci, Matakin da Hukumar kare hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kalubalanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.