Isa ga babban shafi
isra'ila-Falesdinu

Mutane da dama sun mutu a Gaza

Hare haren da dakarun kasar Isra’ila suka kai zirin Gaza da sanyin safiyar yau Asabar, sun yi sanadiyyar mutuwar Palesdinawa 16, lamarin da ya kara yawan wadanda suka mutu a kwanaki 5 da aka shafe anan tashe tashen hankula a yankin zuwa 121. Mai Magana da yawun ma’aikatar lafiya Ashraf al-Qudra, yace Hare haren da aka kai kan masallatai da gidajen shugabannin kungiyar Hamas, sun yi sanadiyyar mutuwar mutanen ne a yankuna daban daban a birnin Gaza.Hukumomin kasar ta Isar’ila sun kuma bayar da umarnin daukar sojojin wucin gadi har 40,000, don taimakawa wadanda ke kasa, tare da barazanar ci gaba da kai hare hare ta kasa. 

Zirin Gaza a wayewar garin yau Asabar
Zirin Gaza a wayewar garin yau Asabar REUTERS/ Amir Cohen
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.