Isa ga babban shafi
Saudiya-Amurka

John Kerry na Amurka zai gana da ‘yan tawayen Siriya a Saudiyya

Sakataren harkokin wajen Amurka john Kerry ya kai ziyara a kasar Saudi Arebiya yau Jumu’a domin ganawa da ‘yan tawayen kasar Siriya akan duba yiyuwar basu tallafin kayan fada na kudi Dollar Amurka Miliyan 500 domin yaki da gwamnatin kasarsu

wikimedia.org
Talla

Baya ga kayan fada na makudan kudaden da kasar Amurka ke son baiwa ‘yan tawayen na kasar Siriya, akwai kuma batun horaswa kan dabarun yaki ga ‘yan tawayen.

An dai shirya cewar Kerry zai hadu da jagoran ‘yan tawayen Ahmad Jarba da yayi jagorancin fadan da aka tafka a baya, tsakanin ‘yan tawayen na kasar Siriya da kuma Sojin gwamnatin shugaba Bashar al-assad.

Haka ma Kerry na shirin ganawa da Sarki Abdallah na kasar Saudi Arebya da ya yi kira ga kasar Amurkan ta taimakawa yan tawayen.

Dama dai gwamnatin Obama ta bada taimakon Dollar Biliyan 2 domin samar da muggan makamai, amma kuma Amurka na shakkun kar kayan fadan su fada a hannun masu tada kayar baya.

Jami’an kasar Amurkar dai na ci gaba da yin gum da Bakinsu, akan cikakken bayani kan ko wadanne samfurin kayan fadan ne Amurka za ta baiwa ‘yan tawayen.

Kasar Amurka dai ta damu da tafiyar Hawainiyar da ‘yan tawayen masu samun goyon bayanta ke yi na rashin iya kifar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Siriya mai samun goyon bayan gwamnati a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.