Ban Ki-moon ya yaba da zaben Afghanistan
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Afghanistan tare da mika sakon taya murna ga mutanen kasar akan samun nasarar gudanar da zaben da kungiyar Taliban ta yi barazanar haramtawa.
Wallafawa ranar:
Mr. Ban ya jinjinawa shugabannin hukumar da suka gudanar da zaben tare da fatar zasu kamanta gaskiya wajen fadin sakamakon da al’umma suka zaba.
Sai dai akwai ‘Yan takara a zaben shugaban kasar da suka yi korafin an yi magudi a zaben.
Hukumar zaben Afghanistan tace ta samu korafe-korafe a game da zaben 1,200.
Barazanar kungiyar Taliban na kai hare haren bama bamai a runfunan zabe bai hanawa Miliyoyan mutanen kasar fitowa kada kuri’arsu ba domin zaben wanda zai gaji Hamid Karzai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu